Kamata yayi wa’adin mulki na biyu kuma na karshe na shugaba Joseph Kabila ya kare nan da mako guda, a ran 19 ga watan nan na Disamba, amma zai ci gaba da zamansa akan karaga a dalilin wata yarjejeiyar da akace an kulla da wani rukuni na ‘yan adawa, wanda zai bashi damar zama a kan kujerarsa ta mulki har zuwa shekarar 2018.
Sai dai mafi yawan jam’iyyun adawa duk sun ki yarda da wannan shirin, suna cewa sai shugaban ya sauka daga mulki a ranar Litinin mai zuwa.
Daga cikin wadanda aka dauki matakan horaswa a kansu din har da mataimakin frayim-ministan Congo din, Evariste Boshab da kuma Kalev Mutondo, shugaban Hukumar Leken Asiri ta kasar.