A zamanin gwamnatin PNDS Tarayya ne aka dauki matakin sassauci don bai wa masu amfani da kafafen sada zumunta cikakkiyar damar morar ‘yancin fadin albarkacin baki kamar yadda dokokin cikin gida da na kasa da kasa suka yi tanadi sai dai da gwamnatin rikon kwarya tace wasu ‘yan kasar ta Nijar na wuce makadi da rawa da sunan wannan ‘yanci.
Matakin da ya haifar da fargaba a wajen‘yan jarida da masu amfani da kafafen sada zumunta.
A watan Yulin 2022 ne Majalissar Dokokin kasa ta wancan lokaci ta dauki matakin hana zartar da hukuncin dauri ga duk wanda aka samu da laifin cin zarafi ta hanyar kafafen sadarwa na zamani don maye gurbin da biyan tara.
A wancan zamani mahukunta sun ayyana matakin a matsayin yunkurin bai wa jama’a damar morar ‘yancin fadin albarkacin baki, to sai dai wasun na fakewa da wanan mataki don yada kalaman batanci da cin zarafi da na yunkurin tada zaune tsaye inji ministan shara’a mai shara’a Alio Daouda a sanarwar da ya fitarta.
Ya kuma kara da cewa lura da wannan aika aika ya sa shugaban kasa Janar Abdourahamane Tiani saka hannu kan wata takardar da ke dauke da wasu sauye sauyei, saboda haka daga yanzu duk wanda aka kama da aikata irin wadanan laifika zai bakuncin gidan yari kai tsaye kuma sabuwar dokar ta tanadi daurin da ka iya farawa daga shekara 1 zuwa 2 ko shekaru 3 har shekaru 5 hade da biyan tarar da ke farawa daga miliyon 1 zuwa million 5 cfa.
Sai dai masu amfani da kafafen sada zumunta na cewa abin ya yi tsanani.
Wannan ya sa wani dan fafutika ta hanyar Blog Mamoudou Djibo Hamani ya yi kira a sake duba batun.
Yace babbar matsalar da ke tattare da wannan mataki shine dazaran aka ce an sameka da laifi ba za a yi maka kowane irin sassauci ba ko a ba ka damar yin kason talala. Ba makawa sai a garkame ka a kurkuku.
"Muna sake aika kira ga shugaban CNSP ya sake duba wannan doka don bai wa ‘yan kasa dama su bayyana ra’ayoyinsu ba tare da wata tsangwama domin wannan doka na barazanar rufe bakunan mutanen da ka iya bada shawarwari masu amfani."
‘Yan jarida na daga cikin wadanda ke nuna fargaba a game da gyaran fuskar da aka zo da shi lamarin da ka iya maida hannun agaogo baya a aiyukan bai wa al’umma labarai na zahirin abubuwan da suka wakana.
Amma a tunanin Shugaban kungiyar ANEPI ta mawallafan jaridu masu zaman kasu Zabeirou Souley magana ce da za iya cewa ta kasu ta rabu.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna