Sabbin alkaluman da hukumar dakile cututtuka ta Najeriya, NCDC ta fitar sun bayyana cewa karin daruruwan mutane sun kamu da cutar COVID-19.
A cewar hukumar, mutum 663 ne cutar ta harba wanda hakan ya mayar da adadin mutanen da suka kamu da cutar zuwa 13,464 a kasar.
Har yanzu dai jihar Legas ce ke kan gaba wajen yawan wadanda ke dauke da cutar, inda yanzu ta sake samun sabbin kamu 170. Sai jihar Ogun da ke bin ta da mutum 108.
Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Bauchi inda aka samu 69, 49 a Ebonyi, 33 a Edo, 30 a Rivers, 26 a birnin tarayya Abuja, 26 a Jigawa, 20 a Delta, 17 a Anambra, 16 a Gombe, 16 a Kano, 15 a Imo, 14 a Abia, 11 a Borno, 11 a Oyo, 8 a Filato, 6 a Kebbi, 6 a Kaduna, 4 a Ondo, 2 a Naija, 2 a Katsina, 1 a Osun, 1 a Ekiti, 1 a Kwara, 1 a Nasarawa.
Hukumar ta kuma bayyana cewa mutum 4,206 suka warke daga cutar yayin da mutum 365 suka mutu.
Facebook Forum