Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Ci Gaba Wajen Kawar Da Matsaloli Tsakanin Manoma Da Makiyaya – Bankin IDB


Islamic Development Bank
Islamic Development Bank

A shekara ta 2022 ne shugaban bankin raya musulinci wato IDB, Dr Muhammad Al-Jasser ya kaddamar da shirin bankin na raya noma da kiwo a jihar Kano da nufin samar da abinci da dakile rikici tsakanin manoma da makiyaya

A karshen makon jiya ne Jami’an Bankin Bunkasa Harkokin Tattalin Arziki a kasashen Musulmai mai shelkwata a birnin Jidda na kasar Saudiyya suka ziyarci jihar Kano, inda suka yaba da irin ci gaban da aka samu wajen aiwatar da ayyukan bunkasa samar da abinci da kawar da fitintunu tsakanin makiyaya da manoma, karkashin tsarin bankin na raya noma da kiwo a kasashe masu tasowa.

Haka dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da reshen jihar Kano na Babban Bankin Najeriya (CBN) ke fayyace gudunmawar sa wajen karfafa gwiwar manoma a jihar ta Kano.

A shekara ta 2022 ne Shugaban Bankin Raya Musulinci wato IDB, Dr Muhammad Al-Jasser ya kaddamar da shirin bankin na raya noma da kiwo a jihar Kano da nufin samar da abinci da dakile rikici tsakanin manoma da makiyaya kana da kuma samar da hanyoyin dogaro da kai a tsakanin al’uma, wadda aka kebe wa dalar Amurka miliyan 95 domin aiwatar dashi cikin shekaru biyar.

Baya ga ganawa da Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf da Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, tawagar jami’an bankin na IDB sun kuma ziyarci yankunan da suka ci gajiyar aikace-aikacen bankin, kana daga bisani suka tattauna da manema labarai.

A cewar, Alhaji Ibrahim Garba Mohammed Gama, Kodinatan aiwatar da Shirin a Kano, ya zuwa yanzu an cimma kusan kaso 80 cikin 100 na aikace-aikacen da aka tsara.

Dangane da matakan dorewa ko wanzuwar shirin bayan karewar wa’adin da bankin ya kebe kuwa, Alhaji Ibrahim Garba Gama yace, “Duk aikace- aikacen da mukeyi na tafiya ne da tsare-tsaren dorewar su, kamar cibiyoyin sarrafa madara guda 100 da muke ginawa, mun samar da kudade na musamman domin bada horo ga wadanda zasu rinka tafiyar dasu. Haka kuma mahautan da muka samarwa da mayanka ta zamani mun hada su da kwararru da zasu koyar da su su kware sosai ta wannan fannin”, a cewarsa.

Habaka madatsun ruwa domin noman rani, samar da cibiyar kula da lafiyar dabbobi ta zamani da kuma cibiyoyin sarrafa madara na daga cikin burikan shirin.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da reshen jihar Kano na Babban Bankin Najeriya CBN ke cewa, dimbin manoma a sassan jihar ne suka ci gajiyar tsare-tsaren bunkasa noma na bankin, kamar yadda Alhaji Umar Ibrahim Biu, Kwanturolan Bankin a Kano ke fadi.

“Dayake ba mune ke bada kudaden kai tsaye ba, amma muna tsaya musu, sauran bankuna su ba su wannan rancen, kana idan aka samu matsala mu biya”, in ji shi.

Abin jira a gani shine yadda wadannan tsare-tsaren tallafi daga hukumomi da cibiyoyin gida dana ketare zasu yi tasiri wajen saukar hauhawar farashin kayayyakin abinci da sauran kayan masarufi da ‘yan Najeriya ke fuskanta.

A saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

An Samu Ci Gaba Wajen Kawar Da Matsaloli Tsakanin Manoma Da Makiyaya – Bankin IDB
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG