A yau Litinin gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da cewa a karon farko an samu wani da ya mutu sakamokon cutar COVID-19 a cikin jihar.
Shugaban kwamitin kula da cutar coronavirus a jihar kuma mataimakin gwamnan jihar, honarable Umar Usman Kadafur ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin 20 ga watan Afrilu. Ya kuma yi wa Muryar Amurka karin bayani inda ya ce mutumin wanda ya kamu da cutar yana aiki ne da kungiyar Doctors without boarder ta MSF (Médecins Sans Frontières), an kuma kai shi asibitin koyarwa na jihar Barno daga Pulka inda ya rasu. Amma an yi masa gwaji inda aka gano yana dauke da cutar coronavirus.
Umar ya kuma ce ya zuwa yanzu an dauki matakan da suka dace, ciki har da killace mutane kusan 97, wadanda suka yi cudanya da mutumin da ya rasu kuma ana kokarin yi musu gwajin cutar.
Sannan kuma ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da kiyaye dukkan matakan da suka dace, kamar kiyaye shiga cunkoso da yawaita wanke hannuwansu.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Haruna Dauda.
Facebook Forum