1. Rikicewa ko kasa magan: Idan mutumin na samun wahala wajen yin magana ko fahimta, abinda ake kira aphasia, zai iya zama cewa jini baya zuwa wannan sashi na kwakwalwa wanda ke lura da harshe. Ka sa mutumin ya maimaita wata magana ta layi daya. Idan yana jan baki ko kuma maganar bata fita, wannan na iya zama alamar matsala.
2. Wahalar gani da tunani: Shanyewra sashi jiki na iya rage kaifin gani na ido daya ko dukan idanuwa ko kuma ya sa a riga ganin abubuwa biyu biyu. Zai kuma iya kawo wa mutum rashin iya gane wasu abubuwa ko mutane, ko kuma matsalar banbanta abinda ya gani na ido ko na madubi.
3. Wahalar motsawa: Rashin iya tsayawa daidai (jin jiri) da kasa tafiya, wannan ya nuna cewa sashin kwakwalwar dake kula da jijiyoyin jikin ya sami matsala.
4. Ciwon kai mai zafi: Ciwon kai mai zafi mara dalili shima alamar shanyewar sashin jiki ne, yawanci irin wannan ya kan sami dangantaka da fashewar jijiyar jini a kai.