Yanzu haka dai a Najeriya ana ci gaba da tabka muhawara a kan batun sake fasalin makomar kasar ta fuskar mulki da zamantakewa.
Tuni ma har wasu jihohi sun amince da su goyi bayan batun sake fasalin kasar, musamman ta fuskar tsarin raba iko tsakanin gwamnatin tarayya da jihohin.
Jihohin dai na ganin kamata ya yi Gwamnatin Tarayya ta bar musu bangarorin lafiya da sufuri da aikin kashe gobara da sauran wasu fannoni, yayin da ita kuma zata mayar da hankali kan harakokin tsaro da na kasashen waje da kuma kudi.
To sai dai kuma yayin ake cigaba da cece-kuce game da wannan batu na sake fasalin kasar, an fahimci cewa a bisa doka ‘yan Majalisar Dokokin kasar ne kawai ke da hurumin duba batun.
To ko wadanne matakai zasu dauka akan lamarin?
Hon.Abdurrazaq Namdas dake zama shugaban kwamitin yada labarai na Majalisar Wakilan Najeriya yace tuni suka kafa kwamitin da zai ji ra’ayoyin jama’a akan dacewa ko rashin dacewar sauya fasalin kasar.
Shima tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa) ya bayyana cewa tsarin da aka gina Najeriya a kansa yanzu yana da matsaloli masu tarin yawa.
Ga rahoton Ibrahim Abdul’Aziz akan wannan batun.
Facebook Forum