Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Ma'aikaciyar Al-Jazeera Da Ta Bace A Syria

Wakiliyar tashar talabijin ta Al-jazeera Dorothy Parvaz
Wakiliyar tashar talabijin ta Al-jazeera Dorothy Parvaz

Tashar talabijin ta Al-Jazeera ta bada labarin cewar ‘yar jaridar dake mata aiki a Syria wadda aka bada sanarwar ta bace a lokacin da take daukan labarun zanga-zangar kin jinin Gwamnatin Syria a watan da ya gabata, yanzu dai ta koma gida Qatar lami lafiya.

Al-Jazeera ta bada labarin cewa a yau laraba, ‘yar jarida Dorothy Parvaz ta isa birnin Doha cikin koshin lafiya. An daina jin Duriyar ‘yar jarida Dorothy ne tun ran 29 ga watan Afrilun da ya gabata bayan da ta isa birnin Damscus.

Jami’an Syria suka ce ‘yar jaridar tayi kokarin shiga Syria ne da fasfon Jabun kasar Iran, don haka suka kamata suka tura Iran domin bincike. Hukumomin Iran din ne suka sakota.

XS
SM
MD
LG