An kara maido da dokar hana fita har ta tsawon sa’o’i 24 a wasu sassan jihar Kaduna.
Sabuwar dokar na zuwa ne bayan kisan da wasu masu garkuwa da mutane suka yi wa wani basarake a masarautar Adara, Dr. Mai Wada Galadima.
“Gwamnatin jihar Kaduna ta maido da dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a garin Kaduna da kewaye.” Inji wata sanarwa dauke da sa hannun mai bai wa gwamna shawara kan harkar yada labarai, Samuel Aruwan.
Sanarwar ta kara da cewa “dokar ta fara aiki daga 11 safe na ranar 26 watan Oktoba 2018, kuma za ta ci gaba da kasancewa har sai yadda hali ya yi.”
“Daukan wannan mataki na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya yayin da muke alhinin mai Martaba AgomAdara.”
A makon da ya gabata aka yi garkuwa da basaraken.
Jihar ta Kaduna ta sha fama da rikice-rikice masu nasaba da addini da kabilanci inda a makon da ya gabata wani rikicin da ya faro daga Kasuwar Magani ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 50.
Facebook Forum