Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Ofishin Jakadancin Najeriya A London Bayan Mutum Biyu Sun Kamu Da COVID-19


Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Mr. Geoffrey Onyeama
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Mr. Geoffrey Onyeama

Ofishin zai ci gaba da kasancewa a rufe har tsawon kwana goma kamar yadda dokar yaki da cutar ta coronavirus ta tanada a Burtaniya.

An dakatar da harkoki tare da rufe ofishin jakandancin Najeriya da ke London a Burtaniya, bayan da aka gano cewa wasu jami’an diflomasiyyar Najeriya biyu sun kamu da cutar COVID-19.

Ofishin zai ci gaba da kasancewa a rufe har tsawon kwana goma.

Hukumomin ofishin jakadancin ne suka bayyana hakan cikin wata sanarwa da suka fitarkamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Sanarwar ta kara da cewa, da tsakar rana, shugaban ofishin kula da fannin shige da fice da wasu jami’ai biyu, sun je wani taro ne inda daga baya aka gudanar da gwajin akansu.

“A kofar shiga, an yi masu gwajin cutar COVID-19, sai aka gano daya daga cikinsu na dauke da kwayar cutar.

“Nan da nan aka kebe shi, sannan sauran jami’an da gwajinsu ya nuna ba sa dauke da cutar za suka kebe kansu har tsawon kwana 10.”

Faruwar wannan lamari ya sa ofishin jakadancin ya sa a yi wa daukacin ma’aikatansa gwaji, inda aka sake gano wani mai dauke da cutar.

“Bisa ka’idoji da yaki da cutar COVID-19 da kuma bukatar ganin an bi sharuddan kasar, ofishin zai rufe har tsawon kwana 10, domin a bi dokar kebe wadanda suka yi mu’amulla da wadannan jami’ai.” Sanarwar ta ce.

XS
SM
MD
LG