Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kulle Jama’ar Afirka Ta Kudu a Gida


Yadda sojojin Afrika ta Kudu ke aiwatar da umurnin zama a gida domin kare yaduwar cutar coronavirus a Afirka ta Kudu. Ranar 27, Maris, 2020
Yadda sojojin Afrika ta Kudu ke aiwatar da umurnin zama a gida domin kare yaduwar cutar coronavirus a Afirka ta Kudu. Ranar 27, Maris, 2020

Yayin da jama’ar Afirka ta Kudu suka shiga yanayi na kulle a gidajensu, hukumomin kasar sun sanar da mutuwar mutum biyu sanadiyyar cutar Coronavirus.

Wannan shi ne karo na farko da aka samu mutuwa a kasar yayin da adadin wadanda suka kamu da COVID-19 ya kai kusan 1,000.

A daren ranar Alhamis aka baza sojoji a titunan kasar domin tabbatar da jama’a sun bi umurnin zama a gida har na tsawon kwana 21.

“Adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai 927 kuma nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, zai iya kai wa 1,500.” In ji Shugaba Cyril Ramaphosa.

Ya kuma kara da cewa, “aikin da ya rataya a wuyanmu shi ne mu kare rayuka, mu kuma rage masu kamuwa da cutar, domin mu maido da al’amura yadda suke a Afirka ta Kudu.”

A ranar Alhamis, miliyoyin jama’ar kasar ne suka dunguma zuwa shaguna domin sayen kayayyakin amfani.

Cikin mako uku da za a kwashe a kulle, babu wanda za a bari ya fita waje sai dai don wani dalili mai matukar muhimmanci kamar sayen abinci ko magani.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG