Labarai daga majiya mai karfi sun bayyana cewa an sami nasarar kubutar da dalibai 340 da aka sace su a makarantar sakandaren kwana da ke garin Kankara ta jihar Katsina a ranar Juma'a da ta gabata.
Rahotannin sun bayyana cewa an sami nasarar kwato wadannan daliban ne a wani yankin jihar Zamfara. Gwamnatin jihar ta Katsina ta tabbatar da cewa yanzu haka wadannan daliban suna hannun karkashin kulawar ta kuma suna cikin koshin lafiya.
Nan ba da jimawa ba ake sa ran gwamnan jihar ta Katsina Alh. Aminu Bello Masari zai karbi wadannan daliban da kuma bayyana wa duniya halin da suke ciki.
Ga rahoton da wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa ya hada muna cikin sauti.
Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, da jihar Katsina.
-
Yusuf Harande
Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.