An kori wasu jami’an ‘yan sanda hudu dake da hannu a kama wani Ba’amurke bakar fata a ranar Litinin, wanda ya mutu bayan da wani jami’in 'yan sanda ya danne masa wuya da gwiwa.
Wani da ya shaida lamarin ne ya dauki hoton bidiyo, ya kuma watsa shi a kafar sada zumunta inda nan take hoton ya karade Amurka baki daya.
Magajin garin birnin Minneapolis, Jacob Frey, ya wallafa sako a shafin Twitter da ke cewa, korar ‘yan sandan hudu daga aikinsu, “abu ne da ya kamata.”
Sunan mutumin da aka kashe George Floyd. Hukumar ‘yan sandan Minneapolis ta ce, ya yi kama ne da wani mutum da ake nema kan laifin damfara, ta kuma ce jami’an sun dauki mataki ne bayan da Floyd ya ki bayar da hadin kai wajen kama shi.
Hoton bidiyon ya nuna yadda wani baturen dan sanda rike da Floyd wanda aka sakawa ankwa a ‘kasa. Dan sandan dake kan Floyd yana fada masa ya kwantar da hankalinsa, amma ya ci gaba da barin gwiwar kafarsa akan wuyan Floyd na tsawon mintoci har ya daina motsi. Wani da ya shaida lamarin ya ce, Floyd yana ta kiran sunan mahaifiyarsa kafin ya mutu.
Facebook Forum