Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Sojan Haya Dan Kasar Romaniya a DRC


Wadansu sojoji suna sintiri a kauyukan da aka kai hari
Wadansu sojoji suna sintiri a kauyukan da aka kai hari

An kashe mutane 3 tare da raunata dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a gabashin Jamhuriyar Damokaradiyar Congo.

Rahotanni na nuni da cewa, an kashe wani "sojan haya" dan kasar Romania da wasu sojojin Congo biyu, sannan wani sojan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ya jikkata a wasu hare hare uku da suka faru a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, a cewar majiyoyi da yawa a jiya Lahadi.

Kasuwa da mayaka suka kai hari a gabashin congo
Kasuwa da mayaka suka kai hari a gabashin congo

Wani jami'in tsaro a gabashin kasar da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, an kashe wani sojan haya, wasu uku kuma sun jikkata a ranar Asabar sakamakon wani hari da makami mai linzami da aka kai kan wani sansanin sojan Congo da ke da nisan kilomita 10 daga arewacin birnin Goma.

Ba a dai tabbatar da musabbabin harin ba.

Wani kauye da aka kai hari a Congo
Wani kauye da aka kai hari a Congo

Tsawon watanni kenan dakarun Rwanda da 'yan tawayen M23 suka yi wa babban birnin North Kivu kawanya daga arewa da kuma yamma.

Ana dai gwabza fada a kai-a-kai da sojojin Congo a wajen birnin, yayin da 'yan tawayen da ke samun goyon bayan Kigali ke ci gaba da mamaye gabashin kasar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG