Jiya talata, a yayinda aka kamalla taron kolin nukiliya, wanda kasashe hamsin da uku suka halarta, wanda kuma batun Korea ta arewa ya kanainaiye, shugaba Barack Obama na Amirka da wasu shugabanin kasashe sun yi kiran da’a dauki matakan yaki da barazanar ta’adancin da makaman nukiliya.
A sanarwar karshe da suka gabatar daga Seoul babban birnin kasar Korea ta kudu, shugabanin kasashe ciki harda shugaban China Hu Jintao da kuma Prime Ministan Pakistan Yousuf Raza Gilani, sunyi kira da’a dauki matakan dakile yadda farar hula ke amfani da ma’adinin uranium da aka karawa inganci sosai, wanda za’a iya amfani dashi wajen kera makaman nukiliya.
Tunda farko a jiya Talata, shugaba Obama yace tilas kasashen duniya su dauki matakan rage yawan makaman nukiliya da aka tara.