An kama mutanen uku ‘yan kasar Ghana a garin Abalak dake jihar Tahoua, dauke da makamai har 30, wadanda aka shigar da su Nijar daga kasar Libiya, dake fama da matsalar tsaro tun lokacin da aka hambarar da gwamnatin Mohammar Ghaddafi.
Gwamnan jihar Tahoua, malam Abdurraham, ya tabbatar da faruwar wannan lamari, inda ya ce jihar Tahoua na fama da ire-iren wannan matsala, domin kuwa kwanaki goma da suka gabata ma, an kama wasu masu fataucin miyagun kwayoyi da makamai. Hakan yasa jami’an tsaro suka kara kaimi a fannin tsaro.
Malam Abdurrahman ya yi kira ga al’ummar jihar da su tashi tsaye wajen baiwa jami’an tsaro hadin kai a wannan aiki da suke yi. Ha-kazalika yayi kira ga direbobin dake ‘dauko haramtattun kayayyakin da akayi fataucinsu domin gujewa fadawa hannu jami’an tsaro.
Jami’an tsaron garin Abalak dai basa kasa a guiwa wajen ganin doka ta yi aiki kan irin wadannan mutane idan suka fada hanu.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Mamman Bako.
Facebook Forum