Wannan samamen da aka kai wurin adana makamai da ke Yimbdi, ya zo ne mako guda bayan da wata kungiyar ta'addanci mai alaka da al-Ka'ida ta kashe mutane akalla 29 tare da raunata wasu da dama, ciki har da wasu 'yan kasashen waje da dama, a wani babban otal da kuma wani wurin shan shayi da ke kusa.
Mai magana da yawun sojin, Willy Youmeogo ya fadi jiya Asabar cewa dukkan mutane 10 da ake zargin su na da hannu a samamen da aka kai wurin adanar makaman, tsoffin dogarawan tsaron fadar Shugaban Kasa ne. Ya ce an kuma kama wani shugaban addini.