'Yan sanda a Rasha sun kama fiye da masu zanga-zanga 100 da ke adawa da yin kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasar da ta yiwu ya ba Vladimir Putin damar ci gaba da kasancewa kan karagar mulki karin shekaru 16, a cewar wasu masu sa ido kan hakokkin bil’adama.
Kimanin mutane 500, galibinsu sanye da takunkumin rufe hanci da baki da aka rubuta kalmar "a'a" wato “No” da turanci a kai, su ka yi tattaki zuwa babban titin Moscow babban birnin kasar ranar Laraba 15 ga watan Yuli.
Wasu kuma sun yi ta daga tutocin da ke bukatar Putin ya yi murabus, yayin da wasu suka kira Shugaban na Rasha "barawo."
Kungiyar sa ido kan harkokin siyasa mai zaman kanta da ake kira OVD-Info, ta bayar da rahoton kamen mutane fiye da 100, amma 'yan sanda da jami'an Rasha ba su ce komai ba tukun.
Facebook Forum