Kimanin sinkin tabar wiwi 155 ne jami’an tsaron garin Tsernaoua suka gano a wata motar daukar marasa lafiya a lokacin da direbanta ke kokarin shigar da su birnin Tahoua, wato akan hanyarsa ta komawa gida daga birnin Yamai inda asibitin Tahoua ya turo shi ya zo da wani mara lafiya da ke cikin mawuyacin hali.
Malan Ganda Saley, shi ne shugaban kungiyar ADENA mai yaki da safarar miyagun kwayoyi, ya ce sun ga wurin da aka dauko kayan aka sa cikin motar. Ya kara da cewa yanzu haka an kama direban kuma sauran wata biyu ya yi ritaya daga aiki. Bincike ya nuna cewa shekaru uku kenan ya na wannan sana'ar.
Faruwar wannan al’amari ya sake farfado da muhawara akan yadda ta’amali da miyagun kwayoyi ke kara karfafa a wannan kasa.
Ali Magasha, ya ce shigowar kwaya ta lalata yara. Duk wani kalubale da a ke fuskanta kamar ta'andanci, ba don komai ba ne ila kwaya.
Ko a makon jiya jami’an tsaro a mashigar birnin Yamai sun kama wata mota dauke da sinkin tabar wiwi 141 lamarin da ya bada damar gano mutane 7 da hannu a wannan aika-aika, cikinsu har da wani alkalin kotun Dosso da mataimakiyarsa, da soja 1 wadanda a halin yanzu ke kulle a gidan kaso kafin a nan gaba su gurfana a gaban kuliya.
Saurari cikkaken rahoton cikin sauti: