Wani mutum da ya maka motarsa a kofar shiga ofishin jakadancin kasar China da ke babban birnin Agentina, ya shiga hannu jiya litinin da daddare.
Ana gudanar da bincike akan hadarin da ya janyo kankalin yan sanda da dama a babban birnin na Agentina.
Yan sanda sun ce ba wanda ya ji rauni har shi direban motar dan shekara 24 da haihuwa.
Jakadan Chinan a Agentina baya ofishin a lokacin da hadarin ya faru.
Rahotanni na nuni da cewa an ga direban a shafukan sada zumunta ya na cewa ya na da masaniya akan COVID -19 kuma ya na neman taimakon ofishin jakadancin.
Wani na kusa da ma’aikatar hulda da kasashen waje ya fadawa kamfanin dillancin labarai na faransa, AFP, cewa direban ya tuka motarsa ne ya rafkawa kyauren kofar shiga ofishin jakandancin bayan da aka ki sauraronsa.
A wani rahotan da ba’a tabbatar ba, jaridar Buenos Aires, ta kasar ta wallafa cewa direban na neman mafaka ne a ofishin jakadancin.
Facebook Forum