Yayin da aka yi kwannaki da kaddamar da dokar zama a gida a wasu jihohi domin takaita yaduwar Coronavirus, wasu batutuwa na kara tasowa kamar na mawuyacin hali da mutane suka shiga, tsadar kayan abinci, ko kuma cin zarafi daga jami'an tsaro.
To shin jama'a na bada hadin kai kuwa?
DSP Suleiman Yahya Nguroje shine kakakin rundunan 'yan sandan jihar Adamawa, kuma ya bayyana wa Muryar Amurka cewa kawo yanzu akwai wadanda suka kama bisa zargin karya doka.
Ya ce “an samu cafke mutum 11 da suka ki bin umurnin wannan dokar, kuma muna da niyyar gurfanar da su gaban kotu.”
Su ma dai talakawa masu karamin karfi, suna ci gaba da kokawa, inda suke cewa a duba halin da suka shiga na yunwa.
Kawo yanzu tuni aka soma zargin jami’an tsaro da wuce gona da iri da kuma cin zarafi da karbar na goro, batun da kakakin rundunan 'yan sandan jihar Taraba DSP David Misal ke cewa ba za'a lamunta ba.
Suma a nasu bangaren, kungiyar kare hakkin Dan Adam ta Centre for Human Rights Advocacy a jihar Taraba na cewa, tuni suka dana tarkonsu na haska irin wadannan jami'an tsaro da ke wuce gona da irin.
Saurari cikakken rahoton a sauti.
Facebook Forum