Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Daruruwan Masu Zanga-zanga Da Suka Mamaye Majalisar Dattawan Amurka


Masu zanga zanga da aka kama
Masu zanga zanga da aka kama

'Yan sandan majalisun dokokin Amurka suka damke masu zanga zanga su 575 akasarinsu mata suna nuna kin amincewarsu da dokar raba yara da iyayebsu da suka shigo kasar ba kan ka'ida ba

An kama daruruwan masu zanga-zanga bayan da su ka shiga tare da mamaye zauren Majalisar Dattawan Amurka a birnin Washington don su nuna rashin amincewarsu da manufofin Shugaba Trump kan shigi da fici.

'Yan sandan shiyyar Capitol sun damke masu zanga-zanga 575, akasari mata, masu yin tir da manufofin ba sani ba sabo na Shugaba Trump kan bakin haure.

Masu zanga-zanga sun rurrufe jikinsu da barguna, irin wadanda aka bai wa yaran da aka raba su da iyayensu a kan iyakar kasar ta kudu.

Sanatoci 'yan jam'iyyar Democrat Tammy Duckworth na Illinois da Maizi Hirono na Hawaii da kuma Ed Markey daga Massachusetts na daga cikin wadanda su ka ziyarci masu zanga-zangar don nuna masu goyon baya.

'Yar Majalisar Dokokin Amurka Pramila Jayapal ta Washington, wadda ita ma zuwa kasar ta yi, ta aika da sako ta kafar twitter cewa ta na tare da wadanda aka kama din. Ta ce, "Yanzun nan aka kama ni tare da mata sama da 500 da su ka taru don kabulanatar manufofin Trump masu tsauri, wanda ba zai dore ba. Ba a kasarmu ba; ba kuma da sunanmu ba."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG