Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Harin Ta'addanci A Kan Jami'an Tsaron Garin Say Km 60 Da Birnin Yamai


Wasu da yan bindiga suka kashe
Wasu da yan bindiga suka kashe

A jamhuriyar Nijer wani harin ta’addanci da aka kai a tashar bincike ta ‘yan sandan garin Say dake a km 60 da birnin Yamai ya haddasa asarar rayukan da suka hada da jami’an tsaro da farar hula.

Hukumomi sun tabbatar da furuwar wannan al’amari kuma tuni suka tura dakaru domin farautar wadanda suka yi wannan aika aika.

Lamarin ya faru ne a wajejen karfe 2 na safiyar litinin lokacin da wasu ‘yan bindiga suka zo cikin mota da babura suka bude wuta akan jami’an tsaron da ke tashar binciken ‘yan sanda a mashigar garin Say na jihar Tilabery.

Wani mazaunin garin jami’in fafutika Sidik Boubacar Bello ya yi wa Muryar Amurka bayani ta wayar tarho.

Yace "wajen karfe 2 da ‘yan mintoci ‘yan ta’adda sun kai hari akan jami’an tsaro inda aka yi musanyar wuta kuma abin al’ajabi maharan sun hallaka jami’in gandun daji 1 sannan ba a san inda dan sanda 1 ya shiga ba yayinda su ma suka yi nasarar kashe dan ta’adda 1."

Wannan al’amari ya jefa jama’a cikin halin zullumi ganin cewa a bara ma an fuskanci irin wannan hari a tashar bincike ta mashigar Say abinda ke kara tabbatar da cewa sha’anin tsaro a gundumar ta Say na da rauni sosai.

A sanarwar da ta bayar a cikin daren jiya ma’aikatar ministan cikin gidan Nijer ta tabbatar da faruwar wannan al’amari. Ta kuma kara da cewa wani hafsan tsaron gandun daji ya rasu dan ta’adda 1 ya mutu sakamakon wannan hari, sannan abin ya rutsa da wasu fararen hula 2 lokacin da jami’an tsaro suka bi sawun mutanen da suka yi wannan aika aika a cewar hukumomi.

Koda yake akwai alamar samun nasarori a ‘yan watannin nan a kokarin murkushe aika aikar ‘yan bindigar da suka addabi jama’a a yankin Tilabery masu bin diddigin al’amura na kwatanta farmakin na jiya litinin a matsayin wata alamar kafar da ‘yan ta’addan Bukina Faso ke amfani da ita don tsallakowa Nijer. Abba Dan Illela na da irin wannan ra’ayi.

A ranar 24 ga watan Oktoban da ya gabata wani harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Tamou na gundumar Say ya yi sanadin mutuwar ‘yan sanda 2 sannan suka kwashi makamai sai dai daukin jiragen saman da hukumomi suka tura ya bada damar fatatakar maharan a dai dai lokacin da suke neman mafaka a wata mahakar zinare lamarin da ya haifar da zazzafar mahawwara inda wa su ke cewa an hallaka wadanda ba su ji ba ba su gani ba. Zargin da hukumomin tsaro ke cewa ba shi da tushe.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

XS
SM
MD
LG