An kafa wani kwamiti na kasa da kasa da zummar kawo karshen shiga sharo ba shanun da kasar Rasha da sauran kasashe masu bin tafarkin murdiya ke yi, a tsarin dimokaradiyyar yammacin duniya.
Kwamitin mai suna Transatlantic Commission on Election Integrity, ko Hukumar Tabbatar Da Ingancin Zabe Na Yankin Atlantic da ma gaba (TCEI) a takaice, da ke karkashin jagorancin hadin gwiwar tsohon Sakatare-Janar din NATO Anders Fogh Rasmussen da kuma tsohon Skataren hukumar tsaron gida ta Amurka Michael Chertoff, ya kira taron manema labarai ranar Jumma’a a birnin Washington DC.
Musabbabin kafa kwamitin shi ne “katsalandan din da Rasha ta yi a zaben Amurka na 2016,” a cewar Rasmussen ga Sashin Rashanci na Muryar Amurka. Ya kara da cewa, “To amma ba kawai game da Amurka ba ne. Har ma da bangaren Turai. Mu a Turai mun fuskanci kalubale, kuma wannan ne ma dalilin da ya za hurumin kwamitin ya zarce yankin Atlantika.” Ya ce akwai zabuka wajen sama da 20 da ke tafe a yammacin duniya gabanin zaben Shugaban kasar Amurka na 2020.
Facebook Forum