Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar da Tsarin Inshorar Takaful da Ya Dace Da Musulunci a Birnin Lagos Na Nijeriya


Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Sanusi Lamido Sanusi
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Sanusi Lamido Sanusi

Yau a birnin Lagos na Nijeriya, Ma’aikatar Kudin Nijeriya ta kaddamar da tsarin inshorar nan na Takaful.

Ma’aikatar Kudin Nijeriya ta kaddamar da tsarin inshorar nan na Takaful, wanda ya dace da addinin Musulunci, amma kuma mai bin kowane addini na iya amfani da shi.

Da ya ke jawabi yau a birnin Ikko wurin kaddamarwar, Ministan Kudin Nijeriya Alhaji Lawal Ingawa y ace wannan tsarin na Takaful ya banbanta da nay au da kullum. Y aba da misalign cewa babu wani ajiyayyen kamfanin insuran da ya mallaki tsarin saboda jama’a ne da su ka hada kansu za su rinka tara kudi karkashin wannan tsarin na Takaful don su rinka taimakon juna idan bukatar hakan ta taso. Hakazalika, Ministan y ace wannan tsarin bai da kudin ruwa tsakanin masu shi, saboda za a rinka raba ribar

kasuwancin ne daidai da abin da mutum ya ajiye. Haka kuma ba za a yi kasuwancin da bai halatta ba da kudin. Sannan kuma, in ji Ministan, kudin da ka zuba na nan a matsayin kudinka ko da kuwa ka fita daga tsarin.

Da wakilinmu, wanda ya turo mana da rahoton ya tambaye shi irin rawar da gwamnati za ta iya takawa sai Ministan ya ce dayake sha’ani ne na haduwar jama’a gwamnati ba za ta shigo sosai ba. Za ta samar da yanayin da zai taimaka ne kawai amma za ta bar jama’a su tafi da harkokinsu yadda su ke so; saidai hukuma za ta bi kadi ma duk wanda aka kwara ko kuma ya ke da korafi.

Shi ma Kwamishinan Inshora na Kasa, Mr. Fola Daniel ya ce ba Musulmi ne kadai za su iya amfani da wannan tsarin ba. Mai bin kowane irin addini na iya amfani da tsarin muddun ya cika sharuddun da jama’a su ka gindaya. Ya kara da cewa za a yi hukunci irin na Musulunci ne ga duk wanda ya saba ma wannan tsarin.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG