Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya shugabanci kwamitin tattalin arziki na kasar zuwa Landan domin haduwa da kungiyoyin kasuwanci da kamfanoni su tattauna yadda zasu saka jari a Najeriya su kuma bunkasa tattalin arzikin kasar. Ziyarar ta kwana uku ce wadda suka soma ranar Laraba. To amma an wayi gari ranar Alhamis sai gashi shugaban ya kamu da wata rashin lafiya da ta yi sanadiyar hana shi ganawa da wadanda ya je dominsu. Ana ganin taron da bai iya zuwa ba zai taimaka wurin samun masu saka jari domin bunkasa tattalin arzikin kasa.
Kakakin shugaban kasan Mr. Reuben Abati ya bayyana wa manema labarai cewa lallai shugaban kasa yana fama da wata 'yar rashin lafiya wadda ta sa kwararru kan fannin kiwon lafiya suka duba shi kana suka bashi shawara ya huta. Ya ce ba wani abu ba ne na damuwa ga 'yan kasa saboda shi da kansa ya ga yakamata ya binciki lafiyarsa.
Amma tuni wasu 'yan Najeriya suka fara nuna damuwarsu domin wai gwamnati tana wani boye-boye dangane da ainihin lafiyar shugaban. Sun ce ba'a taba fitowa fili a fadi irin matsalar da yake da ita ba duk da lokaci-lokaci yana fadawa cikin rashin lafiya da sukan shafi aikinsa na shugaban kasa.
Abokin aiki Sahabo Aliyu Imam da ya yi fira da wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa ya tuna mashi cewa ya ce can baya shugaban ya sha kamuwa da rashin lafiya a kasashen waje. Malam Musa sai ya ce kwarai akwai lokacin da shugaban ya je taron tarayyar shugabannin Afirka a kasar Habasha inda bai iya gabatar da jawabinsa ba ga takwarorinsa domin kamuwa da rashin lafiya. A lokacin ministan harkokin wajen Najeriya ya gabatar da jawabin. A kasar Amurka ma lokacin da ya yi ziyara ya kamu da ciwo. Ya ce irin wannan lamarin yana faruwa lokaci-lokaci don haka 'yan kasa zasu soma tunanin akwai wani abun da ake boye masu.
Ga karin bayani.