Yayinda ake ta shirye-shiryen zaben shekara mai zuwa, kungiyoyin mata a jihar Gombe da suka hada da na addini, sun dukufa wajen fadakar da mata muhimmancin mallakar katin zabe. A halin da ake ciki, kungiyoyin na mata sun kaddamar da shirin shiga gida-gida don tantance matan da basu mallaki katin zabe ba.
Wakilin Muryar Amurka Abdulwaham Mohammed ya yi hira da wasu Shugabannan kungiyoyin FOMWAN da na CAN. Inda suka bayyana masa cewa hakika mata na da rawar da zu taka a al’umma musamman a fannin siyasa kuma sun ce zasu wayar ma mata da kai.
Da aka tuntubi kwamishiniyar mata Hajiya Sa’adatu Mustapha, Alkyabbar Kaltingo, cewa tayi ba ta ji dadin yadda mata da yawa ba su yi rijistar ba amma basu makara ba, don kuwa kuri’un mata na da muhimmanci.