A yayin da jiragen saman yaki na sojojin Najeriya suke ta kai hare-hare a kan 'yan Boko Haram da suka bullo da wani sabon salon buya cikin gidajen mutane fararen hula a garuruwa kamar Michika da Gulak, wani mai sarauta a kasar Mubi ya karyata rahotannin cewa sarki yayi gudun hijira zuwa Yola, babban birnin jihar.
Dan Ruwatan Mubi, John Elias, yace Mai Martaba Sarkin Mubi, Alhaji Abubakar Ahmadu, shi ne Amirul Hajj na mahajjatan Jihar Adamawa a bana, kuma yana Yola tun shekaranjiya domin ganawa da maniyyatan tare da tattaunawa da su.
Cif Elias yace babu wani tashin hankalin dake faruwa yanzu haka a cikin Mubi, kuma babu wani dalilin da zai sa sarkin barin garinsa. Ya kara da cewa sarkin zai koma Mubi idan ya kammala aikin da tuntuni aka shirya zai gudanar.
A halin da ake ciki kuma, sojojin Najeriya da jiragen saman yaki su na can su na farautar 'yan Boko Haram, musamman a garin Michika, inda 'yan tsageran suka bullo da wani sabon salo na lallashin jama'a da kada su gudu.
Mazauna garuruwan da suka samu tserewa suka ce 'yan bindigar su na gudu su buya cikin gidajen fararen hula a duk lokacin da suka ji karar jirgin saman soja dake farautarsu a sama.
Haka kuma an ce su na fasa kantunan da aka kulle su na fitar da abincin da suke rabawa jama'ar da suka tsaya ba su gudu ba, tare da sanyawa ana girkawa a ba su su ma.