Wani shahararren Sheihin malamin boko a China, mai yawan sukar yadda gwamnatin China ke ma 'yan kabilar Uighur tsiraru, zai gurfana a gaban kotu a yau dinnan Labara, saboda tuhumarsa da ake yi da laifin yada akidar aware.
Ilham Tohti Sheihin Malami ne (wato furfesa) a fannin tattalin arziki ne kuma sanannen mai kare muradun al'ummarsa, wadanda akasari Musulmi ne, wadanda su ka jima su na kokan an danne su a yankin yamma mai nisa na Xinjiang.
Tohti, wanda ya musanta zargin yada manufar awaren, na fuskantar yiwuwar daurin rai da rai muddun, kamar yadda ake zato, Kotun da ke Urumqi, hedikwatar wannan yanki mai fama da tashin hankali, ta same shi da laifi.
Ganin sarkakkiyar wannan al'amarin, 'yan sanda sun dakatar da 'yan jarida da wasu jami'an diflomasiyyar Yammacin Duniya da dama daga zuwa kusa da kotun, inda ake shari'ar shi Tohti.
An kama Tohti ne a watan Janairu sannan daga baya kuma aka zarge shi da laifin bada goyon baya ga ta'addanci da akidar aware a jawabansa da rubuce-rubucensa da kuma irin abubuwan da ya ke rubutawa a kafafen yada labarai na kasashen waje.