Zangar zangar ta wakana ne yayin da wasu jihohin Amurka suka kafa dokar-ta-baci sakamakon zanga zangar da ta jirkice take komawa tarzoma a wasu sassan kasar – wacce ta samo asali daga jama'ar da suka fito domin nuna fushinsu, kan George Floyd – bakar fatar na mai shekara arba'in da shida, da ya mutu yayin da ‘yan sanda suka rike da shi.
Sai dai zanga zangar ta birnin Gaithersburg da ke karamar hukumar Montegomery a jihar Maryland ta gudana ne cikin lumana.
Na tuntubi wata ba'amurkiya farar fata, wacce ta halarci wannan gangami, na kuma tambaye ta dalilinta na fitowa a wannan rana.
"Sunana Jessica, mijina Ba'amurke ne bakar fata, dukkanin yara na amurkawa ne kuma bakaken fata, wannan abu ne da na mutakar yadda da shi sosai.”
Shi ma a nashi bangaren Mr Chris Hall, wanni mutumin wanda shi ma ya fito zangar zangar cewa ya yi:
“Ina ga wannan hakkin ne da ya rataya a wuyana, na shiga wannan zanga zanga, saboda na koyawa yarana (wato yaki da matsalar wariyar launin fata) zan kuma so ya zama darasi da za a rika koyarwa a makarantu.”
Masu zanga zangar, bai wai kawai sun fito ne domin nuna fushinsu kan yadda ‘yan sanda ke muzgunawa bakaken fata ba ne, har da ma yadda ake nuna wariyar launin fata ta wasu hanyoyin da dama a duk fadin Amurka.
Sabanin sauran wasu wurare da zanga zangar ta jirkice ta koma tarzoma, an kammala gangamin na Gaihersburg ba tare da wani tashin hankali ba.
Saurara karin bayani a sauti:
Facebook Forum