An gudanar da zaben zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki da kuma shugabannin kananan hukumomi a kasar Tanzaniya a zaben da aka ce za a fi kowanne fafatawa a tarihin kasar.
Jam’iyar CCM da ta dade bisa karagar mulki, tana fuskantar matsin lamba, da neman ta gaggauta daukar makatan habaka kasar da shawo kan talauci da ya yi Kamari, sai dai masu fashin baki sun yi harsashen cewa, jam’iyar ce zata sake lashe zabe.
Ministan ayyuka na kasar Tanzani John Magufuli shine dan takarar jam’iyar CCM. Jam’iyar hamayya ta zabi tsohon Firai minister Edward Lowassa a matsayin dan takararta.
Shugaban kasa mai ci yanzu, Jakaya Kikwete zai kamala wa’adin mulkinsa da kundin tsarin mulkin kasar ya kayyade. Shugabannin kasar Tanzaniya sun shiga tarihi wajen kiyaye wa’adin mulki, ba kamar sauran kasashen nahiyar Afrika ba.
A kasar Ivory Coast kuma,shugaban kasa mai ci yanzu Alassane Quattara da ake kyautata zaton zai sake lashe zabe yace yana son ya sami gagarumar nasara a zagayen farko.
Ana ganin zaben da ake gudanarwa yau Lahadi a matsayin zakaran gwajin dafi a kasar da tayi fama da tashin hankalin bayan zabe shekaru biyar da suka shige, da ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane dubu uku.
‘yan takara shida suke kalubalantar shugaban kasar dan shekaru 73, yayinda wadansu hudu suka janye bisa zargin shirin tafka magudi.
Al’ummar Jamhuriyar Congo kuma sun je runfunan zabe yau domin kada kuri’ar raba gardamar da gwamnati ta shirya da nufin cire sashen da ya kayyade wa’adin mulki biyu ga shugaban kasa, wanda kuma shekarunsa ba zai shige saba’in ba a lokacin da yake neman tsayawa takara.
Masu hamayya da Nguesso dan shekaru 71 sun yi kira ga masu kada kuri’a su kauracewa kuri’ar.
A cikin hirarsu da Ibrahim ka-Almasih Garba, Dr Usman Bugaje yace zabukan alama ce ta ci gaba da ake samu a kasashen nahiyar Afrika a fannin damokaradiya.
Ga bayanin Dr Bugaje .