Jiya Lahadi ‘yan kasar Mali suka yi zaben fidda gwani na shugaban kasa. An gudanar da zaben ne cikin tsauraran matakan tsaro domin dakile duk wata tarzoma. Yan kasar na Mali sun yi zaben ne tsakanin ko su sake maida shugaba Ibrahin Boubacar Keita akan wani wa’adin shekaru biyar ko kuma su maye gurbinsa da Saumalia Cisse.
Ana ci gaba da kidaya kuri’u a wasu rumfunan zabe dubu ashirin da uku bayan da aka kamalla zabe da misalin karfe bakwai na maraice. A zagaye na farko na zaben da aka yi shugaba Keita dan shekara saba’in da uku ya samu kashi arba’in da biyu daga cikin dari na kuri’un da aka kada, tsakanin yan takara ashirin da hudu, idan aka kwatanta da kashi goma sha takwas daga cikin dari na kuri’un da Cisse dan shekara tamanin da takwas ya samu, wanda shugaba Keita ya doke a zabe da aka yi a shekara ta dubu biyu da goma sha uku.
Zagaye na farko na zaben ya fuskanci hare haren da aka dora laifinsu aka ‘yan jihadi ciki harda wadanda aka danganta da kungiyar Al Qaida da kuma ISIS, da kuma tarzomar kabilancin data tilasta aka rufe daruruwan runfunan zabe.
Gwamnatin kasar ta dauki tsauraran matakan tsaro a zaben na fidda gwani da aka yi jiya Lahadi ta tura sojoji dubu shidda hade da dubu talatin wadanda tuni suke bakin aiki.
To amma kuma duk da matakan tsaron da aka dauka an kashe wani jami’in zabe a yankin Timbuktu dake arewacin kasar aka kuma kona wani rumfan zabe kamar yadda wata kungiyar nazarin zaben mai suna Citizen Observation Pool of Mali, wadda take da masu lura fiye da dubu biyu ta baiyana. Haka kuma kungiyar ta bada rahoton aukuwar wasu al’amurra a jiya Lahdi
Kungiyar ta kuma ce, a arewa da tsakiyar kasar Mali fiye da rumfunan zabe hamsin ne suka rufe kafin tsakar rana a saboda barazanar masu ra’ayin rikau.
Facebook Forum