Zai ci gaba da kasancewa kan karagar mulki na tsawon shekaru 2 lokacin da za a gudanar da babban zaben kasar.
Majalisar tattaunawar wanda 'yan adawa da kungiyoyin fararen hula suka kauracewa, itace ta amince da bai wa shugaba Deby damar tsayawa takara lokacin gudanar da zaben, duk da alkawarin da yayi lokacin da ya karbi mulki cewar ba zai tsaya takara ba.
Bikin dai ya samu halartar shugabannin kasashen Afirka cikin su harda Muhamadu Buhari na Nigeria.