A Jamhuriyar Nijar, an fara rijistar masu zabe a yau Asabar 8 ga watan Fabrairu, a jihohin Maradi, Damagaran, Diffa da Niamey.
Bayan da aka kammala irin wannan aiki a wasu jihohin kasar hudu, wato Agadez, Tahoua, Tilabery da Dosso, an ci gaba da shirye-shiryen zaben na gama gari wanda za a gudanar a shekarar 2020 da 2021.
‘Yan kasar kusan million 5 ne ake saran yi wa rajista a wadanan jihohi da kasashen da kasar ke da ofisoshin jakadanci a yayin wannan aiki da ke matsayin zango na biyu na ayyukan da hukumar zabe ta kaddamar.
Shirin na kokari ne ya samar da kundin rajistar da zai ba da damar ba da katin zabe mai hoto da zanen yatsu.
Darekta mai kula da ayyukan rijista a hukumar zabe ta CENI, Malam Oumarou Saidi, ya yi kira ga ‘yan kasar akan muhimmancin ‘yin wannan rjista.
Firim Minista Birgi Raffini, ya jagoranci kwaryakwaryan bikin da aka shirya a ma’aikatar Magajin Garin Yamai domin kaddamar da wannan aikin yin rijistar.
Wannan shi ne karon farko da za a fara amfani da katin zabe mai hoto da zanen yatsu a Jamhuriyyar Nijar.
Ministan cikin gida Bazoum Mohamed, ya ce wannan matakin zai magance dukkan wani yunkurin murda zabe.
A karshen watan Nuwamba ake sa ran gudanar da zaben kananan hukumomi, yayin da za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasa a watan Disamba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Facebook Forum