Gwamnatocin Arewacin Najeriya sun fara gudanar da tsarin mayar da Almajirai zuwa jihohinsu na haihuwa daga jihohin da suke zaman ci rani da kuma karatu.
A karon farko jihar Bauchi ta karbi Almajirai 196 daga jihar Plateau.
Mukaddashin gwamnan jihar Sanata Baba Tela shi ne ya karbi Almajiran, inda ya ce, sun karbi Almajiran tare da maluman su 7, kuma gwamnatin jihar za ta killace su, a tabbatar da lafiyarsu kafin a mayar dasu wurin iyayensu.
Ya ce ita ma gwamnatin jihar Bauchi ta fara nata shirin na mayar da duk Almajiran da ke jihar zuwa jihohinsu na asali.
Ita ma gwamnatin jihar Gombe ta mayar da Almajirai 700 zuwa jihohinsu na asali.
Kwamishinan ilmi na jihar, Dr. Habu Dahiru she ne ya gudanar da tsare-tsaren mayar da Almajiran, inda kuma ya yi bayanin yadda aka gudanar da shirin. Ya ce, gwamnatin jihar ta tanadi motoci, abinci da ‘yan Sandan da zasu raka Almajiran zuwa jihohin.
Saurari Karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum