Hukumar da ke hana yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya, ta ce an samu karin mutum 64 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar.
Hakan ya sa a yanzu ana da jimullar mutum 1,337 da ke dauke da cutar kenan a duk fadin kasar.
"Ya zuwa karfe 11:20 na daren ranar 27 ga watan Afrilu - an tabbatar mutum 1337 ke dauke da #COVID19 a Najeriya." NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter.
Hukumar ta kuma kara da cewa, jihar Legas ta samu karin mutum 34, 15 a birnin tarayya na Abuja, 11 a Borno, sai kuma jihohin Gombe da Taraba da kowannensu ya samu mutum biyu.
A cewar hukumar, bayan mutum 64 da suka kamu da cutar, ba a samu rahoton mutuwa ba cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Sannan kuma babu wata sabuwar jiha da aka samu bullar cutar.
Mutum 40 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar, sannan an sallami 255 a cewar NCDC.
Facebook Forum