A ranar Laraba 13 ga watan Nuwamban 2019, aka fara gasar kwallon kafa ta tunawa da Sir Ahmadu Bello Sardaunar Sokoto wacce ake yi duk shekara a yankin Arewacin tarayyan Najeriya kuma wannan shi ne karo na bakwai.
Gasar, mai taken: All Temers Sardauna Northern Veteran's Football Competition, jihar Bauchi ce a bana ta dauki nauyinta kuma jihohi 12 ne su ke fafatawa, kuma sun hada da Jihar Gombe wacce ta karbi bakuncinta a shekarar da ta gabata, kuma ita take rike da kambun gasar.
Sauran jihohin da suka halarci gasar sun hada da Plateau, Borno, Sokoto, Kebbi, Kano Katsina Benue, Zamfara da Niger, sai jihar Bauchi masu masaukin baki. Jihar Adamawa bata samu damar zuwa ba sabo da wasu dalilai.
'Yan wasan kwallon kafa masu shekaru sama da arba'in ne suke kece raini a tsakaninsu.
Shugaban shirya gasar a kasa Mr Biomi George ya ce ana shirya gasar ne domin tuna da Sir Ahmadu Bello Sardauna bisa irin gudunmawar da ya bada kasa da kuma samun hadin kan juna a tsakanin tsofaffin 'yan wasa na Arewa, yanda suka fafata a matakin jiha da kasa da kuma kasashen duniya
Wasan, wanda zai dauki tsawon kwanaki hudu ana yi za a kammala shi a ranar Asabar 16 ga watan nan da mu ke ciki.
Shugaban shirya gasar a matakin jihar Bauchi, Billy Tafawa Balewa, ya, ce sun kammala dukkannin shirye shirye na ganin an yi wasan lafiya ba tare da samun matsala ba.
Facebook Forum