An tura jami'an tsaro zuwa masallatan idi dake manyan biranen jihar domin kare rayukan masallata.
Amma an kira jama'a da su sa ido a masallatan da suke saboda gano duk wani da basu yadda dashi ba. Haka ma jama'a su lura da wuraren hada-hadar jama'a.
Daukan matakan tsaron nada nasaba da rahotannin sirin da hukumomin tsaro ke cewa sun samu game da barazanar kai hari ko kunar bakin wake a masallatai musamman a wuraren hada-hadar jama'a.
Saidai hukumomin tsaro sun bukaci jama'a da su kwantar da hankulansu amma su sa ido akan kawo komo da jama'a keyi da zummar ba jami'an tsaro rahoton abun da basu yadda dashi ba.
Kakakin rundunar 'yansandan jihar DSP Joseph Kwaji ya bayyana irin matakan da suka dauka game da bukuwan sallan. Yace akwai jami'an tsaro da zasu tabbatar an yi sallah lafiya.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.