Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bukukuwan Sallah: An Dau Matakan Kare Sansanonin ‘Yangudun Hijira


Wasu 'yan gudun hijira a jahar Borno
Wasu 'yan gudun hijira a jahar Borno

Hukumomin da abin ya shafa na cigaba da ba da tabbacin cewa su na daukar matakai daban-daban na ganin an yi bukukuwan Sallah lafiya lau.

Yayin da ake harmar bukukuwan Sallah, hukumomi a Najeriya sun ce suna kan daukar matakan da su ka dace don kare ‘yan gudun hijira musamman ma wadanda ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijiran daban-daban.

Wakilinmu a shiyyar Adamawa Ibrahim Abdul’aziz ya ce tuni ma aka kara yawan sojoji da ‘yansanda a sansanonin. Ya ruwaito babban jami’in hukumar NEMA mai kula da sansanomnin ‘yangudun hijira da ke jahar Adamawa, Alhaji Sa’ad Bello na cewa hatta yadda ake saka ido da kuma bincike ya karu a harabar sansanonin. Y ace baya ga sojoji da ‘yansandan da aka kara, an kuma kara yawan ‘yan sintirin sa-kai.

Alhaji Sa’ad y ace baya ga kara ingancin matakan tsaro, an kuma hada kai tsakanin hukumar NEMA ta SEMA ta jahar wajen samar da kayan more rayuwa ma ‘yan gudun hijirar saboda su yi bukukuwa cikin anashuwa da kwanciyar hankali. Ibrahim y ace wasu jiga-jigan jahar Borno sun je don yin bukukuwan Sallar da su saboda karfafa masu gwiwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

XS
SM
MD
LG