Hadaddiyar Kungiyar masu saida kayan abinci da dabbobi a Najeriya, ta bada sanarwar dakatar da yajin aikin da ta shiga na tsawon kwanaki, don hana mambobinta kai kayan abinci da dabbobi kudancin kasar.
Wasu da ke bayyana ra'ayinsu jim kadan bayan sanarwar dakatar da dokar, suna cewar, hakan yayi musu dadi, don kuwa mutanen kudancin kasar a yanzu sun fahimci muhimancin mutan arewacin kasar.
Sai dai a bangare daya kuwa, wasu na ganin cewar an yi saurin bada kai bori ya hau, kamata ya yi sai an dauki lokaci mai tsawo don su kara fahimtar cewar rayuwar kowa bata yuwuwa sai da taimakon juna. Taron gwamnonin arewa da na kudancin kasar sun taka rawa wajen cinmma wannan matsayar.
Duk kuwa da cewar Hausawan sun yi nasara akan samun izinin maida kasuwarsu wani bangare, wanda suka ce ba za su koma tsohuwar kasuwar ba, hakan zai ba su damar cin gashin kansu a tasu kasuwar.
Wata 'yar kasuwa ta ce hakan bai yi daidai ba, don an ce za a karbo musu 'yancinsu, amma a nata ganin wannan ba shi ne abun da su ke bukata ba, suna bukatar a ce Fulani makiyaya da Hausawa suna iya yawo cikin walwala ba tare da tsangwama ba, kamar yadda 'yan kudu ke da 'yancin yin haka a jihohin arewacin kasar.
Don samun karin bayani cikin sauti, sai a saurari rahoton Hassan Umaru Tambuwar a cikin sauti.
Karin bayani akan: Fulani, Hausawan, Nigeria, da Najeriya.