‘Yan kasuwar kayan gwari da nama da sauran kayan abincin da ake shigowa da su daga arewaci zuwa kuduncin Najeriya, sun shiga yajin aikin ne domin nuna rashin jin dadin su da abin da suka kira kashe ‘ya’yan su da kuma lalata masu dukiya sakamakon zanga zangar Endsars da kuma fadan kabilanci da aka yi a kasuwar SaSa da ke jihar Oyo a kwanakin baya.
Malam Malami Jos mai sayar da dankakin turawa ne a kasuwar Mile 12 da ke jihar Legas ya ce sun dauki matakin neman gwamnati ta biya su diyya na fiye da Naira miliya 400 a kan asarar da su ka yi.
Wata matar aure mai suna Iya Ramatu ta ce kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabi, saboda da matakin yajin aikin da ‘yan arewa ‘yan kasuwa ke yi na kashe musu ‘yan uwa da lalata kaya, kuma ina goyon bayan su.
Ramatu ta kara da cewa yanzu haka farashin atarugu da su ke saya kwando daya dubu shida ance ya koma dubu 16, haka ita ma albasa da ake sayar da ita kasa da dubu 10 ya koma kusan dubu 30.
Alhaji Umar Atina wani mai gidan abinci ne a unguwan Agege ya ce yana goyon bayan matakin yajin aikin domin haka zai sa ‘yan kudu su san muhimmancin ‘yan arewa nan gaba domin su dai na wulakanta su.
Sai dai yayin da kungiyar ‘yan kasuwar suka ja daga, tuni an fara daukan matakan sasanta wa tsakanin bangarorin biyu.
Saurari cikakken rahoton Babangida Jibril:
Karin bayani akan: Umar Atina, jihar Oyo, Nigeria, da Najeriya.