Hukumar lafiya ta Duniya ta cire kasar Indiya daga jerin kasashen dake fama da cutar shan inna ranar asabar, yayinda cutar take ci gaba da kasancewa annoba a Najeriya da Pakistan da kuma Afghanistan, abinda ya zama wata gagarumar ci gaba ga ma’aikatan lafiya dake kokarin shawo kan cutar dake gurguntar da yara.
Firai Ministan kasar Pakistan Manmohan Singh ya bayyana farin ciki da cewa, “wannan ya bamu karfin guiwa cewa, zamu iya kawar da cutar shan inna ba a Indiya kadai ba amma a duniya baki daya.”
Da wannan sanarwar, adadin kasashen da cutar ta zama annoba sun ragu zuwa uku, da suka hada da Najeriya da Pakistan, da kuma Afghanistan.
Indiya da ta shafe sama da watanni goma sha biyu ba tare da samun wani yaro dauke da cutar ba, zata dauki tsawon shekaru biyu ana sa ido kafin ayyana kasar a matsayin wadda ta shawo kan cutar shan inna baki daya. Bisa ga cewar wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya a Indiya Natela Menabde.
Firai ministan kasar Indiya ya bayyanawa wani taron yaki da cutar shan inna da aka gudanar a birnin New Delhi cewa, gwamnatin kasar Indiya ta kaddamar da wani gagarumin shirin yaki da cutar da nufin raba kasar da cutar da ta tsorata dubun dubatan rayukan kananan yara a kasar Indiya.
Sai dai yace an sami nasarar shawo kan yaduwar cutar polio ne a kasar Indiya sabili da mika wuyan ma’aikatan sa kai da suka rika yiwa yara rigakafi. Bisa ga cewarshi, ma’aikatan sa kai sun shiga kowanne lungun kasar Indiya da tashoshin jiragen kasa, da wuraren ayyukan gini, da tashoshin mota, suka kuma yi amfani da kowanne irin abin tafiya wajen isa dukan lungunan kasar da ta kasance daya daga cikin wadanda suka fi cunkoso da talauci a duniya.
Bisa ga cewarshi, nasarar shirin ya nuna cewa, hada hannu yana kai ga cimma nasara.
Cutar shan inna wadda take kama kananan yara da shekarunsu basu kai biyar ba, wadda take kisa, ko sa mutuwar gabobi ko kuma gungunta kafa, tana yaduwa zuwa kasashen ketare a cikin sauki ta wajen mu’amala da bayan gidan wanda yake dauke da cutar.
Indiya ta sha yada cutar a kasashen ketare, yayinda ita ma ta rika dauka daga wadansu kasashe. An shawo kan cutar a kasashe masu tasowa wajen shekara ta dubu da dari tara da saba’in ta wajen gangamin allurar rigakafi.
A shekarar dubu biyu da tara kasar Indiya ke da rabin adadin wadanda ke dauke da cutar shan inna a duniya, amma adadin ya ragu zuwa 42 a shekara ta dubu biyu da goma yayinda ba a sami ko yaro daya da cutar ba cikin watanni 12 da suka shige.
Gwamnatin kasar Indiya a kasha dala biliyan biyu cikin shekaru goma zuwa sha biya da suka shige a yunkurin kawar da cutar baki daya a kasar.