Kimanin mutane 1,000 suka yi maci a Kenosha ta jihar Wisconsin a ranar Assabar, a karkashin jagorancin iyalan bakar fatan da ‘yan sanda suka harba, a fafutukar neman kai karshen cin zarafin da ‘yan sanda ke yi a birnin na tsakiyar yammacin Amurka.
Shugaba Donald Trump zai ziyarci birnin a ranar Talata, domin tattaunawa da jami’an hukumomin tsaro da kuma kiyasin al’amarin, a cewar wani jami’in fadar Shugaban kasa ta White House.
Jacob Blake Sr., wanda sashen hagu na jikin dan sa ya mutu sakamakon harbin da wani dan sanda farar fata ya yi masa a makon jiya, ya yi kira ga masu zanga-zangar da su yi ta cikin lumana, kuma su kaucewa tashin hankali.
Dangin Blake da ‘yan fafutuka ne suka shirya zanga-zangar, a yayin da dakarun tsaron kasa suke gefensu a cikin shirin ko-ta-kwana, domin hana barkewar tashin hankali da ya soma aukuwa a Kenosha a farkon makon sakamakon harbin da aka yi.
Jami’in ‘yan sandan Kenosha Rusten Sheskey ya harbi Jacob Black dan shekaru 29 da haihuwa har sau 7 a baya a ranar 23 ga watan Agusta kuma a gaban mutane da suka shaidi lamarin, ciki har da ‘ya’yan Blake kanana, a cewar rahoton ma’aikatar shari’a ta Wiskonsin.
Harbin ya sa birnin mai yawan jama’a 100,000 akasari duk fararen fata, kasancewa wuri na baya-bayan nan na zanga-zangar da ta karade kasar, akan zargin muzgunawar ‘yan sanda, da kuma nuna wariyar launin fata a kaikaice.
Facebook Forum