Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da ceto mutane 6 ciki har da malamai biyu, da aka sace a jami’ar birnin tarayya Abuja da aka fi sani da UNIABUJA.
Jami’an tsaro sun kubutar da mutanen ne kimanin kwanaki uku bayan wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba suka kai hari a rukunin gidajen ma’aikatan jami’ar da ke karamar hukumar gwagwalada.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta fitar a ranar Juma’a inda ta tabbatar da cewa, tawagar hadin gwiwa daga hukumomin tsaro daban-daban ne suka ceto mutanen 6 kamar yadda gidan talabijan na Channels ya ruwaito.
A cikin sanarwar, rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta sanar da jama’a cewa duk wadanda aka sace a jami’ar Abuja an ceto su tare da sada su da iyalansu ta hanyar hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro inji Josephine.
A cikin wadanda aka yi garkuwa da su da jami’an tsaro suka ceto akwai malamai masu matsayin farfesa biyu, babban malami 1 da kuma ‘yan uwansu uku.
Shugaban kungiyar malaman jami’o’i wato ASUU reshen jami’ar ta Abuja, Dakta Kasim Umar, ya tabbatar da cewa an ceto wadanda abin ya shafa kuma ya bayyana cewa ba'a biya kudin fansa ba.
A ranar Talatar makon nan ne wasu ‘yan bindiga suka kutsa cikin rukunin gidajen manyan ma’aikatan jami’ar Abuja da misalin karfe 1 na safiya, inda suka yi awon gaba da mutanen 6.
Majiyoyi daga gwagwalada sun yi nuni da cewa an kwashe sama da sa’o’i biyu ana harbin bindiga a yayin kai hari.
Idan ana iya tunawa ma a ranar Larabar da ta gabata an sami labarin yan bindiga sun shiga rukunin gidajen malamai na makarantar karamar sakandare dake yankin Yebu na karamar hukumar Kwali inda suka yi awon gaba da mataimakin shugaban makarantar, Nuhu Muhammad.