Gwamnan lardin Chiang Rai, Narongsak Osatanakorn, shugaban aikin ceto yace masu nikayya suna bukatar a kalla sa’oi goma su sake shirin rukunin aikin ceto yaran na gaba kuma ana kyatata zaton komi zai tafi da kyau fiye da yadda aka zata.
An kai yaran hudu da aka ceto asibiti. Tun farko jagoran aikin masu aikin ya bayyana cewa, "A shirye muke. Yauce ranar gudanar da wannan aikin. A daidai karfe uku na rana agogon GMT kwararrun nikayya goma sha uku suka shiga kogon suka fara aikin ceto rayukan ‘yan kwallon. Tawagar ta hada da kwararrun nikayya na rundunar mayakan ruwan Thai biyar. Sun tsara yadda zasu shiga kogon da kuma aikinda kowanne dayansu zai yi."
Tawagar ta kunshi kwararrun ‘yan kasashen ketare goma sha uku da kuma fitattun masu nikayya na kasar Thailand biyar, wadanda suke da kwarewar tunkarar kowanne irin yayani da zasu fuskanta.
Kwararrun masu nikayya biyu zasu raka kowanne yaro. Jami’ai sun ce ana kyautata zaton za a dauki kwanaki biyu zuwa hudu kafin a fito da dukan yaran.
Facebook Forum