Wasu ‘yan Nijar sun fara bayyana bukatar ganin hukumomi sun yi wa jama’a bayani, game da abubuwan dake kunshe a rahoton wani bincike da aka gudanar, a ma’aikatar tsaron kasar kan wasu kudade.
Babbar mahawara ta barke a kafafen sada zumunta, bayan bayyanar wata murya da ake alakantawa da sabon ministan tsaron Nijar Farfesa Issouhou Katambe ya yi, wanda alamu ke nuni da cewar an nada a sace ne.
A lokacin da yake yi wa wasu bakinsa bayanin abinda binciken ya gano a ma’aikatar tsaron kasar, a kokarin gwamnati na zakulo masu hannu a aika aikar da ake gani ita ce ta janyo koma baya a yakin da kasar ke gwabzawa da ‘yan ta’adda a watannin baya.
Alhaji Nassirou Seidou, shugaban kungiyar farar hula ta Voix des Sans Voix, ya ce asiri ne ya tonu, tunda babu kaya kuma babu kudin, saboda haka an ci amanar kasa.
Wata tawaga ta musamman ce gwamnatin Nijar ta aika a kwanakin baya, zuwa kasashen Rasha, Ukraine, China da Isra’ila, domin tattaro bayanan da suka shafi wasu kwangilolin jiragen yaki, da makamai da aka ce an bayar don ci gaban wannan yaki da ke lakume kashi 15 zuwa 17 na kasafin kudaden kasar a kowace shekara.
Har yanzu gwamnatin Nijar ba ta yi bayani a hukumance ba, dangane da rahoton binciken, mai sharhi akan ala’muran yau da kullum Abdorhamane Alkassoum na ganin damka abubuwa a hannun kotu ita kadai ce hanya mafi gaskiya.
Ministan tsaron Nijar Farfesa Issouhou Katambe, bai yi bayani akan wannan rahoton bincike ba a lokacin da ofishin Muryar Amurka dake birnin Yamai ya tuntube shi, domin a cewar sa ya riga ya kammala aikin da ya rataya a wuyansa. Ministan ya kuma tabbatar da cewa a boye aka dauki muryarsa.
A saurari rahoto cikin sauti daga birnin Yamai a Jmahuriyar Nijar.
Facebook Forum