Babban hafsan Hafsoshin dakarun kasar Laftanat Janar Farouq Yahaya yace yakin basasar kasar ka iya zama zakaran gwajin dafi ga Askarawan kasar musamman kalubalen da aka fuskanta a wancan lokaci na rashin iya jigilar isassun kayan aiki zuwa filin daga da ma rashin isassun makamai.
Laftanar janar Farouq Yahaya wanda Manjo Janar AB Ibrahim ya wakilce shi yace kai kayayyakin da dakaru ke bukata shine kashin bayan cin nasarar duk wani yaki .
Yace wahalhalun dake tattare da samarwa dakaru makamai daga kasashen waje musamman irin sharruddodi da ka'idoji masu tsauri na daga cikin irin kalubalen dake yin tarnaki ga dakarun Najeriya
Tunda farko saida kwamandan kwalejin horasda dabarun yakin ta Najeriya Manjo Janar Solomon Odounwa yayi bayanin cewa taron zai tattauna dalla-dalla da kuma yin bitar yadda aka gudanar da yakin basasar Najeriya da zummar zakulo mahimman darussan da za a iya dauka don tunkarar kalubalen tsaro da ake fuskanta a kasar a halin yanzu.
An dai gabatar da kasidu daban daban yayin wannan taron, inda masanin tsaro kuma babban malami a jami'ar Jos Farfesa Shedrack Best yayi bayani kan cewar shekaru hamsin da kammala yakin basasar to kuwa lalle akwai darussan da yakamata a koya.
Shehin malamin yace da ya kyautu ace yanzu Najeriya na kera makamai a cikin gida batare da dogara da kasashen wake ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: