Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Taron Kungiyar Kasashen Nahiyar Afrika A Nijar


Yau Alhamis 4 ga watan Yuli ake soma taron kungiyar kasashen Afrika AU, a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar.

Taron wanda a karo na 33 ya tattara shugabannin kasashe Afrika da na gwamnatocin wannan nahiya, taron zai dauki lokaci don tattauna mahimman matsololin da suka hada da tattalin arziki, tsaro, zuwa ci ranin matasa, da dai sauran su. Saboda haka masana a fannoni daban daban ke fatan ganin taron ya fito da shawarwarin da zasu taimaka a samu mafitar matsalolin dake damun jama'a.

Yarjejeniyar kasuwanci ta Zlecaf na kan gaban mahimman abubuwan da shuwagabannin kasashe da na gwamnatocin Afrika zasu mayarda hankulla akan su, a lokacin wannan haduwa ta birnin Yamai wacce a karshen ta ake fatan fara cire damuwar dake dabaibaye harkokin cinikayya a tsakanin kasashen wannan nahiyar, matakin da manyan ‘yan kasuwa ke ganin yana tattare da dimbin alheri.

Wakilin muryar Amurka ya samu hira da jin ta bakin Alhaji Yacouba Dan Maradi, shugaban kungiyar SIEN masu shige da fice.

Tashe tashen hankulan da ke kara yawaita a kasashen Afrika a ‘yan shekarun nan sanadiyar kafuwar kungiyoyin ta’addanci wani kalubale ne, dake damun shuwagabanin nahiyar. Saboda haka masana sha’anin tsaro irin su Farfesa Issouhou Yahaya na jami’ar Yamai ke shawartar mahalarta taron akan bukatar fito da sabuwar dabara.

A kan kwararar matasan Afrika zuwa wasu nahiyoyi domin ci rani na daga cikin matsalolin da ake yiwa kallon mafarin rikice-rikice da ake fama da su a wannan zamani na bazuwar makamai. Dalili kenan jami’in fafutika na kungiyar FSCN Abdou Elhadji Idi, ke ganin ya zama wajibi taron na kungiyar AU ta nemo mafita.

kwararu a fannin tattalin arziki ne zasu share fage a wannan taro na tsawon kwanaki 5, wadanda bayan nazarce nazarce za su gabatarwa ministocin kasashen nahiyar ta Afrika shawarwarin da zasu zo da su, ciki har da yunkurin fito da hanyoyin samarda kudade, bayan nan shugabannin kasashe da na gwamnatoci su saka hannu akan takardun abubuwan da suka yi na’am da su.

Ga rahoton Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG