Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bankado Wata Badakalar Cin Hanci da Aka Kitsa a Majalisar Dinkin Duniya a New York


Babban Sakataren MDD, Antonio Guterres
Babban Sakataren MDD, Antonio Guterres

Wasu tsoffin jami'an Majalisar Dinkin Duniya ne lokacin da suke New York suka kitsa cin hancin da rashawa domin wani kamfanin makamashin kasar China ya samu walwalar yin kasuwanci a nahiyar Afirka

Wata badakalar cin hanci da rashawa da aka kitsa a zauren MDD dake birnin New York wadda kuma ta bazu zuwa wasu nahiyoyi.

Chi Ping Patrick Ho, ‘dan asalin kasar China da Cheikh Gadio tsohon ministan harkokin wajen Senegal, sune suka kitsa baiwa wasu manyan jami’an Afirka cin hanci domin samarwa wani kamfanin makamashi na Shanghai damar gudanar da kasuwanci.

Wadanda suka auna, ya hada da Idriss Deby shugaban kasar Chadi maiarzikin Man fetur, da Sam Kutesa ministan harkokin wajen Uganda wanda kuma ya taba rike mukamin shugaban taron MDD na shekarar 2014 zuwa 2015.

Ranar Asabar aka kama Patrick Ho, aka kuma gurfanar da shi gaban Alkali jiya Litinin, a cewar wata sanarwa da ma’aikatar Shari’a ta fitar jiya Litinin.

Shi kuma Gadio, wanda ya taba rike mukamin ministan harkokin waje na Senegal daga shekarar 2002 zuwa 2009, an cafke shi ranar Juma’a a birnin New York aka kuma gurfanar da shi a kotu ranar Asabar. Yanzu haka dai dukkan su suna tsare.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG