Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa 'Yan Asalin Afrika Da Suka Tsaya Takara a Zaben Amurka 


Yinka Faleti, dan Afrika da ke takara a zaben Amurka 2020.
Yinka Faleti, dan Afrika da ke takara a zaben Amurka 2020.

Yayin da Amurka ke shrine gudanar da zabuka ciki har da shugaba kasa wasu Amurkawa 'yan asalin Afirka su ma sun tsaya neman takara a matakai daban-daban.

Yinka Faleti daga Legas Najeriya da ya tsaya takarar a jihar Missouri ya sha gwaggwarmaya kafin ya kai ga wannan matsayin.

Ya dawo Amurka ne yana dan shekara bakwai, bayan shekaru da dama sai ya samu mukami a Makarantar Sojin Amurka a West Point, makaranta mafi daukaka ta sojoji.

Ya yi aiki na shekara shida a matsayin sojan da ke kula da kayan yaki da ya hada da zuwa aikin soja sau biyu a yankin Gabas ta Tsakiya.

Amma bayan ya bar soja, ya fita da digiri na Lauya kuma yana aikin zaman kansa a matsayin mai daukaka kara a matakin jiha, wani abu na daban ne ya saka shi neman ya ba da gudumawa.

A shekarar 2014 wani harbi da aka yi wa matashi Micheal Brown da wani jami’in dan sanda ya yi a Ferguson, Missouri shi ya tunzura Faleti ya fara nazarin yadda zai ba da gudunmowa.

Yana so ya taimaka wajen kawo daidaito da yake gani a cikin al’umma.

Ya fadawa VOA cewa, “na fara gane matsaloli da dama da muke aiki a kai yayin da muka maida hankali akan wancan batun, sai na fuskanci zaren a matakin jiha ya tsaya.” “ina bukatar na shiga matakin jiha, shi ya sa na shiga takarar takamaimai mai neman sakataren jiha, domin ta nan ne za’a yi yakin dimokradiya a jiharmu.”

Faleti na daya daga cikin Amurkawa masu tushen Afrika guda 15 da suka tsaya takara a Amurka.

Kamar sauran, batutuwan da ke cikin Kampe din Faleti wadanda suka shafe su ne.

Yana bukatar ya sama wa Missouri karin damar kuri’u kuma da batun kada kuri’u. Amma yana fatan takararsa za ta zaburar da wasu na nesa da na kusa.

A baya-bayan nan, ya samu sako daga wani matashi a nahiyar Afrika wanda ya kalli bidiyon yakin neman zabensa, ya ce wannan ya ba shi karfin gwiwa.

Ya ce, “ wannan ya tayar mini da hankali a yanayi na musamman da mutun zai yi tunani a wani yanki na duniya akwai wani matashi da ya kalli bidiyo na mintuna biyu kuma ya samu karfin gwiwa ba don kanshi kawai ba amma don matasa kamarshi a Najeriya da suke ganin idan har zai iya yin haka, to mu ma za mu iya.”

“Ra’ayin na shi ne zan iya samun nasara. Zan iya samun nasara a wannan yanayi na yanzu, a ko wane irin yanayi ne. Wannan ya dada zaburar da ni ya ba ni karfin gwiwa sosai.”

Ngozi Akubuike, 'Yar asalin Afrika da ke takara a zaben Amurka 2020
Ngozi Akubuike, 'Yar asalin Afrika da ke takara a zaben Amurka 2020

Ngozi Akubuike, ‘yar takarar neman kujerar babban alkalin Kotun Gunduma a Ramsey a Minnesota, haifaffiyar Najeriya ce amma labarinta ya sha banban da na baya.

Ta fara aikin lauya a kasarta Najeriya sai ta zo Amurka bayan da ta ci gasser lottery.

Ta ce, “labarin na ba mai sauki ba ne, amma na yi wa wannan ‘yar jaririyar alkawari. A gaskiya wannan rashin mazauni ba shi ba ne karshen rayuwarmu. Saboda haka sai na koma makarantar kwarewar lauyoyi, wato Law School.”

Bayan ta rike mukamai na mai gabatar da kara, da Mai Gudanarwa, da Manajan Shari’a, na dokar da ke bai wa Amurkawa masu bukata ta musamman kariya, wato a Minnesota, Ngozi Akubuike ta ce tana son ta kai abin da ta kware a rayuwa kujerar Alkalai.

Ta ce, “na zabi in koma makaranta ne domin in koyi tsarin kuma na ci gaba a layin kwarewa ta na yi wa al’umma hidima. “kuma kullum na kan gayawa jama’a cewa babu abin da za ka kware akai ya zama mara amfani. Na kan gayawa mutane cewa duk wahalar da za ka sha ‘akwai dalilin yin haka. Na yi imani na shiga wadannan matsalolin rayuwa ne don in koyi wani abu.”

Akubuike ta ce kwarewar ta a rayuwa, ta nuna mata mutane na da 'yancin daidaito akan hukunci.

Ganin cewa ta fuskanci rayuwa ta bangaren marasa galihu, Akubuike ta yi imanin za ta kawo wannan tausayin a kan harkar aikin Alkalanci

Ta ce, “muna bukatar mutane daga bangarorin rayuwa daban-daban, mutanen da suka fuskanci rayuwa masu yawa. Muna bukatar mutane daga kowane matakin rayuwa su zo mu hadu domin mu kawo kanmu daidai da al’ummar da mu ke yi wa aiki."

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG